Monday, July 22, 2024
HomeENTERTAINMENTKira ga masu shirya shirin fim mai dozon zango “series”yaki karewa –...

Kira ga masu shirya shirin fim mai dozon zango “series”yaki karewa – Adam A Zango

Adam a zango yayi kira ga furodusoshi da dakaktoci akan Jan Shiri mai dogon zango yaki karewa

Fitaccen jarumin nan adam a zango yayi kira ga masu shirya fina finai furodusoshi da dakaktoci akan jan Shiri mai dogon zango “series” yaki karewa jarumin yayi bayyanin abinda yasa yayi wannan furuci majiyamu ta samu wannan bayani daga faifan bidiyon da shafin kannywood a facebook sunka wallafa.

Idan bazaku manta shima jarumin yana shirya shiri mai dogon zango tare da fitowa a cikin wasu fina finai irin a duniya da yayi ƙaurin suna da gidan badamasi yayi wannan kira ne domin irin hasashen da yake na masu kallo da kai mai shirin fim ɗin.

Ga abinda yake cewa:

“Wannan sakon na fim yan fim ne da masu kallon baki daya akwai wani kuskure da mukeyi a cikin shiri mai dogon zango a duk lokacin da mutum ya fito, ya fito da niyar yayi zango biyu ma’ana 1 da 2 to amma idan ya karbi a wurin yan kallo wanda sai kaje kayi ta kirkiro wasu abubuwa daga baya ka taɓata fim din baki daya.

Yan kallo su fara tunanin ina fim din ya nufa saboda a duk lokacin da fim din bashida hanyoyin kirkiro abubuwa a cikinsa wanda kayi wannan gobe kayi wannan abubuwan ga su nan to bakin nan maimakon a yaba maka sai a fara korari ina fim dinka ya nuna”.

Adam a zango ya kara da cewa:

“To ni shawara a nan itace ga abokaina masu shiri fim mai dogon zango ‘series’ mu daure mu rika hakuri komai karbuwa da yayi in yazo karshe, muyi wani saboda idan munce muyi ta kawo wani abu dan muna samun kuɗi ko muna burge dan kallo za’a wayi gari ba sakamako mai kyau.

Da a ce turai ne inda kana da yadda zaka gane adadin yawan masu kallonka idan sun ragu zaka gane cewa an ragu da wasu daga cikin mu sun gane abinda nake magana, saboda ni ina bibiyar irin wannan wurare, suna gane adadin mutane nawa suke bina idan sun karu zasu gani idan sun ragu zasu gani.

kuma komai kyaun fim idan sun gamashi sun gamashi amma idan ya zamo yan kallo ne suka duma da yawa zasu iya ƙara zango daya su rufe shi, saboda yan kallo suna son abinda muke yi ne. ba irin namu da mutum zai iya fara daga zango na daya har zuwa goma wanda idan zaka tsaya ka fara kallo daga zango na farko zuwa na ƙarshe zaka samu matsaloli da kura kurai wanda shi mai fim din bazai iya kare kansa ba.

saboda haka yana da kyau mugyara domin indan anyi abunda ya dace za’a ce kannywood tayi nasara, idan akasin haka zaka ce kannywood.

dan allah ayi hakuri idan wani yaji na ɓata masa rai aka abinda na fada”- inji adam a zango.

RELATED ARTICLES

Most Popular

Recent Comments